Kiwon Lafiya
Manyan Jam’iyyun siyasan Najeriya sun bukaci hukumar INEC da ta ba su damar cigaba da yakin neman zabe
Biyo bayan tirjiyar da manyan jam’iyyun kasar nan biyu suka yi na APC da PDP kan cewar ya zama wajibi a basu dama su ci ga ba da yakin neman zabe, a nan gaban kadan hukumar zaben ta kasa INEC za ta zauna a yau domin bibiyar al’amarin
A cewar jami’in yada labaran hukumar ta INEC Rotimi Oyokanmi hukumar za ta zauna ne a yau ta kuma tattauna kan batun, ta kuma yi nazarin ko za ta basu damar ko akasin haka
Manyan jam’iyyun biyu dai sun zargi hukumar ta INEC da cewar hana su ci gaba da yakin neman zaben baya bisa doron doka.
A don hakan ne jam’iyyun suka bukaci hukumar ta INEC da ta bibiyi matakin da ta dauka ta kuma basu damar ci gaba da yakin neman zaben, kamar yadda doka ta basu dama su gudanar.
An dai jiyo manyan jam’iyyun na cewar su kam za su ci gaba da yakin neman zaben su ko da hukumar ta INEC ba ta gamsu ba