Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Marasa kishin Kano ne suka farmaki ‘yan wasan Katsina United-Pillars

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta musanta cewar magoya bayan ta ne suka farmaki motar ‘yan wasan Katsina United, a fafatawar da suka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a ranar Asabar 16 ga Afrilu a gasar firimiya ta kasa NPFL.

Jami’in hulda da jamaya na kungiyar Lurwanu Idris Malikawa Garu ne bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.

Malika “Ya ce wasu bata gari ne da basa kishin Kano ne suka ai kata wannan abu, amma ba magoya bayan kungiyar mu ta Kano Pillars ba,”

A ranar Asabar dai ana tsaka da wasan rahotanni sun bayyana ba a kai ga kammmala wasan ba alkalin wasa ya busa tashi a minti na 89 sakamakon hayaniya da ta barke a filin wasan.

Lamarin da ya kai ga hutuna sunyi nuni da tadda aka farfasa motar ‘yan wasan Katsina United.

Sai dai kuma wannan ba farau bane yadda wasan hamayya tsakanin Kano Pillars da Katsina United baa fiya kammalawa ba tare da an samu rikici tsakanin magoya bayan kungiyoyin Biyu ba.

Kafin a fafata wasan ranar Asabar dai sama da shekaru biyu kenan tun bayan bullar cutar Covid-19 rabon da Kano Pillars ta buga wasa a gida, duba da gwamnatin Kano ta mayar da wajen sansanin killace masu dauke da cutar Covid-19.

Lamarin da ya sanya Kano Pillars komawa jihar Kaduna filin wasa na Ahmadu Bello a matsayin san sanin ta na gida kana ta koma ta koma jihar Katsina.

To amma kamfanin shirya gasar Firimiya na kasa LMC a makon da muke ciki, ya amince da Kano Pillars ta dawo buga wasan ta a filin wasa na Sani Abacha, dake Kofar Mata a matsayin na wucin gadi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!