Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mun amince Kano Pillars ta dawo Sani Abacha da buga wasa-LMC

Published

on

Kamfanin shirya gasar firimiya na kasa LMC ya amince kungiyar kwallon ta Kano Pillars ta dawo ci gaba da fafata wasa a filin wasa na Sani Abacha da Kofar Mata a Kano.

Sanarwar hakan na zuwa ne bayan da sakataren hukumar Alhaji Salisu Abubakar ya sanyawa hannu mai dau keda kwanan watan 12 ga Afrilun 2022 da muke ciki.

Salihu Abubakar ya ce hukumar ta LMC ta karbi korafe-korafe tin daga 1 ga watan da muke ciki daga bangarori da dama na bukatar Pillars ta dawo ci gaba da wasa a Jihar Kano wanda ya ke nan inda zata rika karbar bakuncin kungiyoyi daban-daban.

Kano Pillars dai ta shafe tsahon lokaci ba ta buga wasa a filin Sani Abacha, inda ta koma jihar Kaduna filin Ahmadu Bello kafin daga bisani ta koma Katsina filin Muhammadu Dikko wanda ta ke karbar bakunci wasanni a cikinsa.

Yanzu haka dai Kano Pillars zata kece raini da Katsina United a wasan NPFL a mako mao zuwa da ake saran idan ta kammala shiri tsaf zata buga wasa a filin na Sani Abacha.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!