Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mariri Market Cup: Layin Auwalu Ragabza ya yi nasarar zuwa wasan kusa dana karshe

Published

on

A Ci gaba da gasar cin kofin Mariri Cola Nut Market, da ake kira da Chairman Cup, wasan da aka buga jiya tsakanin kungiyar kwallon kafar Layin Auwalu Ragabza  da Layin Aminu Na Gwagwa.

Layin Aminu Na Gwagwa ya yi rashin nasara a hannun Layin Auwalu Ragabza da ci 2-0.

Dan wasan Layin Auwalu Ragabza Auwalu Sina, ne ya ci kwallayen a mintuna na 5 da 50 da fara wasan.

Nasarar da Layin Auwalu Ragabza ya samu ya bashi damar zuwa wasan na kusa dana Karshe a gasar.

Mai horas da ‘yan wasan Layin Auwalu Ragabza Sadam Yakubu, ya nuna farin cikinsa sakamakon nasarar da suka samu na zuwa wasan na kusa dana karshe.

Shi kuwa mai horas da ‘yan wasan Layin Aminu Na Gwagwa Musbahu Gaye ya ce ”ita dama kwallo farace da baka, a domin haka mun karbi sakamakon da muka samu hannu biyu.

A gobe Lahadi 10 ga watan Oktobar 2021 za’a ci gaba da gasar tsakanin FC Tasha da Layin Sabo Currency duk a kasuwar ta Mariri.

Wasan da za’a take da misalin karfe 4 da rabi na ranar a filin Sakandaren Mariri.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!