Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Laliga: Samuel Chukwueze ya zama dan wasan Afrika na 2 mafi tsada

Published

on

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles dake wasa a kungiyar Villareal dake kasar Spain Samuel Chukwueze, ya zama dan wasa na 2 mafi tsada daga cikin ‘yan wasan Afrika dake wasa a gasar Laliga kasar Spain.

Dan wasan mai shekaru 22 ya fara wasa a kungiyar ta Villareal a shekarar 2017.

Ya kuma buga mata wasanni 119 da ci mata kwallaye guda 17 tare da bayar da taimakon cin kwallaye da dama a wasanni daban-daban.

Chukwueze ya zama dan wasa na 2 ne da darajar sa ta kai Yiro miliyon 30, inda dan wasan kasar Morrocco Youssef En-Nesyri dake wasa a kungiyar Sevilla darajar sa ta kai Yiro miliyon 40 da ya kasan ce na 1.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!