Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mariri Market Cup: Layin Bashir Roja ya yi canjaras da FC Kwata

Published

on

A ci gaba da gasar cin kofin kasuwar Mariri Mai taken Mariri Cola nut Market Cup da ake Kira da Chairman Cup.

A wasan da aka buga yau Lahadi 19 ga watan Satumbar shekarar 2021, tsakanin kungiyar Layin Bashir Roja da FC Kwata an ta shi wasa kowanne layi na da kwallo 3 a zare, wanda hakan yasa aka tashi chanjaras da ci 3-3.

Dan wasan Layin Bashir Roja Salisu Dogo ne ya fara zura kwallo a mintuna na 11 da fara wasa sai kuma dan wasa Adnan ya ci kwallo 2 a mintuna na 23 da 28 wanda hakan ya bawa layin Bashir Roja nasarar zura kwallayen 3.

Mariri Market CUP: Yin wasanni tsakanin ‘yan kasuwa zai samar da hadin kai-Salisu Auwal

Daga bangaren FC Kwata kuwa dan wasa mai suna Namaka ne ya ci gida a mintuna 25 sai Buhari ya ci a mintuna na 30, inda shima Salisu Dogo da ya ci gida dab da za’a tashi daga wasan, hakan yasa aka tashi wasan da ci 3-3.

Da yake jawabi bayan kammala wasan mai horas da ‘yan wasan kungiyar Layin Bashir Roja Bilyaminu Yahuza da ake Kira da tsoho raka ya ce “kurakuran da ‘yan wasan sa suka samu shi yasa aka warware kwallaye 3 da ya zuba a zare, amma duk da haka zamu fito daga wasan Rukuni”.

Shima mai horas da ‘yan wasan FC Kwata Muhammad Adamu ya ce “ba karamin kokari ‘yan wasansa su ka yi ba wajen warware kwallayen da aka sa musu a zare”.

Za’a ci gaba da gasar a ranar Juma’a 24 ga watan Satumbar da muke ciki ta shekarar 2021.

Tsakanin Layin Auwalu Ragabza da Layin Aminu Na Gwagwa da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!