Labarai
Martani: Ƴan kasuwa su yanke hulɗar kasuwanci da ƴan Kudu – CNG
Gamayyar ƙungiyoyin Arewacin ƙasar nan CNG sun buƙaci yan Arewa da suke kasuwanci a yankin kudu da su yanke hulɗar kasuwanci tsakanin su, kamar yadda ƙungiyar ƴan aware Biafra ta umarci al’ummar ta na su daina hulɗar kasuwanci da yan Arewa.
Mai magana da yawun ƙungiyar Sulaiman Abdul’aziz ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da ya aikowa Freedom Radio, da ke matsayin martani ga ƙungiyar IPOB kan hana al’ummar ta daina cin naman shanu waɗanda ƴan arewacin ƙasar nan suke kaiwa Kudu da ma daina yin taken Najeriya.
“Ai muma ƴan Arewa muna da kishin juna, kuma suma ƴan Kudun suna da kayan su a nan, suna kasuwancin su don haka muke kira ga ƴan Arewa da su ƙauracewa sayan kayan su”.
“Yan Arewa da ke kasuwanci a Kudu su ɗauki matakin daidaita kasuwancin su don gudun tafka asara, amma mu ba za mu yarda da irin wannan ba, domin kuwa take-taken su na nuna cewa za su fara farwa ƴan Arewa da ke zaune a can” a cewar Sulaiman.
Ya ƙara da cewa, matakin da suka ɗauka na nuni da yadda suke son tayar da zaune tsaye.
Sulaiman Abdul’aziz ya kuma ce, batun daina amfani da taken Najeriya da ƙungiyar ta IPOB ta hana al’ummar ta, wannan tsakaninsu da gwamati ne.
You must be logged in to post a comment Login