ilimi
Masaratar Kano ta jaddada bukatar samar da makarantun Islamiyya a Karkara

Hakimin Gwarzo Kano Sarkin Dawakin Mai Tuta, Alhaji Muhammad Bello Abubakar, ya ce, samar da makarantun Islamiyya da kuma ingantattun malamai zai taimaka wajen tarbiyya da yada Ilimin addinin musulinci a yankunan karkara da birane.
Sarkin Dawakin Mai Tuta, ya bayana hakan a taron Bude Makarantar madarasatul tajawidul Qur’an Li Bala Muhammad Giwa Getso da za a fara karatun da Dalibai Hamsin Maza da mata, da ya gudana jiya a Garin na Getso.
Hakimin na Gwarzo Muhammad Bello Abubakar,ya kara da cewar Bude makarantar kalubalen ga dalibai malamai da kuma Iyaye dama sauran Al’umma wajen tabbatar da cimma burin da aka sa a gaba na bunkasa Ilimin Addini musamman ga matasa da Kannan yara.
A nasa jawabin wanda ya samar da makarantar Alhaji Bala Muhammad mai lakabin Giwa Getso, bayyana makasudin Samar da makarantar yayi da nufin matso da ilimin addini kusa da al’umma musamman yaran marayu da kuma masu karamin karfi.
Taron bude Islamiyyar ya samu halartar mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam da tshohon Sakataren gwamnatin Kano Alhaji Abba Dabo da Dagatai da masu unguwanni da sauran hukumomin tsaro na karamar hukumar ta Gwarzo.
You must be logged in to post a comment Login