Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masarautar Ƙaraye ta dakatar da dagacin Madobawa daga muƙamin sa

Published

on

Mai martaba sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na II ya dakatar da dagacin Madobawa Malam Shehu Umar daga mukaminsa.

Hakan na cikin wata sanarwar da mai magana da yawun masarautar Haruna Gunduwawa ya fitar ga manema labarai.

Sanarwar ta ce an dakatar da dagacin Malam Shehu Umar ne sakamakon rashin nuna da’a da karfa-karfar da yake nunawa mutanen da yake wakilta.

Kazalika sanarwar ta ce an wakilta Magajin Garin Karaye Injiniya Shehu Ahmad a matsayin wanda zai wakilci kwamatin da aka kafa, domin bincikar dagacin.

Sarkin na Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na II ya umarci Magajin Garin na Karaye da ya wakilta wanda zai ci gaba da kula da kujerar dagacin ta Madobawa.

Kazali sanarwar ta ce an dakatar da Sarkin Kasuwar Karaye Alhaji Sa’adu Abdulkadir har zuwa wani lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!