Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Barka Da Hantsi

NITDA: Fasahar sadarwa na ci gaba da bunƙasa tattalin arziƙi a ƙasar nan

Published

on

Hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta zamani ta ƙasa NITDA ta ce, fasahar sadarwa na taka muhummiyar rawa wujen bunkasa tattalin arziki a kasar nan da ma duniya baki daya.

Shugaban hukumar Kashifu Inuwa Abdullahi ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom radio da mayar da hankali kan gudummuwar da fasahar sadarwa ke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin.

Kashifu Inuwa Abdullahi ya ce zuwan annobar korona ya dada zaburar da mutane Wajen yin amfani da fasahar sadarwa wanda hakan ya taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arziki a kasar nan.

Kazalika ya ce, “A lokacin annobar harkokin fasahar sadarwa ya samu tagomashi, domin kuwa mafi yawan al’amura an mayar da shi kafar internet sakamakon dokar kulle”.

Kashifu ya kuma ce “Wannan ne ya sa gwamnati ta fitar da tsare tsare domin bunkasa  fasahar zamani, haka kuma sabon tsarin nan na 5g zai taimaka wajen bunkasa fasahar zamani da tattalin arziki, kuma nan gaba kadan za mu dora Najeriya akai wanda tuni kasashen da suka ci gaba sun wuce wurin”.

Kashifu Inuwa Abdullahi ya ce hukumar tana bada gudummawa matuka wajen inganta harkar ilimi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!