Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masarautun Kano za su lakume naira miliyan 100 cikin kasafin kudin shekarar 2021

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce masarautun Kano hudu za su lakume Naira milayan 100 cikin kasafin kudin bana domin kawata su.

Kazalika an ware miliyan dari biyu domin daga darajar asibitocin masarautun hudu da suka hadar da: Rano Karaye Bichi da kuma masarautar Gaya duk a cikin kasafin shekarar 2021.

Kwamishinan ma’aikatar kasafin kudi da tsare tsare na jihar Kano Nura Muhammad Dankadai ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai ga me da kasafin kudin shekarar 2021.

Nura Muhammad Dankadai ya kuma ce, cikin kasafin kudin an ware naira miliyan 64 don ginawa masu tallace-tallace akan titi, a wani yunkuri na kawo karshen wahalar da suke sha a yayin gudanar da sana’o’insu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!