Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masari ya gargadi kungiyoyi kan su kauracewa sansanonin ‘yan gudun hijira

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta gargadi kungiyoyi masu zaman kansu da su kauracewa shiga sansanonin ‘yan gudun hijiran da ke fadin jihar.

Gwamnan jihar Aminu Masari ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyara gani da ido daya daga cikin sansanonin fadin jihar, mai suna Faskari Camp.

A cewar Masari, duk da cewa har yanzu akwai bukatar gwamnatinsa ta kara kaimi wajen yakar masu tada zaune tsaye, za ta iya kula da ‘yan gudun hijiranta a sansanon daban-daban na jihar.

Masana ya kuma ce, nan bada jimawa gwamnatinsa za ta hada ‘yan gudun hijran da iyalansu, sannan ta wadata su da isasun abunci da suturu da kuma magunguna, don kara inganta lafiyar su.

A don haka, a cewar masari kungiyoyi masu zaman kansu su kauracewa shiga sansanonin ‘yan gudun hijiranta ba tare da zinin gwamnatin jihar ba.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!