Kiwon Lafiya
Mashaƙo: Za a fara allurar riga-kafin Diphtheria a Kano
Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano ta ce, za ta yiwa mutane miliyan ɗaya da dubu ɗari Biyar allurar rigakafin cutar Mashako da aka fi sani da Diptheria.
Matakin ma’aikatar lafiyar na zuwa ne yayin da mutane ɗari da goma sha shida suka kamu da cutar a wannan lokaci kuma suna ci gaba da karɓar magani a sibitocin da aka keɓe su a nan Kano.
Kwmishinan lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusif ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Juma’a.
Yayin taron Dakta Abubakar Labaran ya ƙaddamar da gangamin allurar rigakafin da za a fara gobe Asabar a wasu kananan hukumomin jihar Kano.
Ya kuma buƙaci iyaye su tabbatar an yiwa yaran nasu rigakafin tare da ɗaukar matakan kariya.
Yayin taron ya samu halarta ƙungiyoyi da hukumomi a fannin kiwon lafiya.
Abba Isah Muhammad
You must be logged in to post a comment Login