Labarai
Masu babbaka su dena amfani da tayoyi –Sarkin tsaftar Kano
Sarkin tsaftar jihar Kano Alhaji Ahmad Ja’afaru Gwarzo ya gargadi masu babbakar kawunan dabbobin da aka yi layya a wannan lokaci na sallah da su guji amfani da tayoyi da tsofaffin robobi wajen babbake kawunan don kuwa yana da illa ga lafiyar jiki da ma muhalli.
Alhaji Ahmad Ja’afaru Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin zantawa da freedom radio a yau.
Ya ce, sun lura masu aikin babbakar suna amfani da tayoyi wajen hura wutar babbake kawunan a don haka da su guji wannan dabi’a don kuwa hatsari ne ga lafiya.
Gwarzo ya Kuma ce, akwai sinadarai masu illa a jikin tayoyin da idan an yi amfani da ita wajen babbake kawunan zai haifar da cutuka masu illa ga jiki.
Alhaji Ahmad Ja’afaru Gwarzo ya ce za su dauki matakan ladabtarwa ga wadanda suke sabawa dokokin tsaftace muhalli musamman a wannan lokaci da duniya me fuskantar kalubale na annoba.
You must be logged in to post a comment Login