Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masu bukata ta musamman 9 ne ke shirin karbar takardar kama aiki a matakin gwamnatin jihar Kano

Published

on

A yau ne mutane masu bukata ta musamman su 9 za su karbar takardar kama aiki a matakin gwamnatin jihar Kano.

Tun da fari dai masu bukata ta musamman su 134 ne suka nemi aiki a matakai daban-daban a nan Kano.

Sai dai a zantawar da Freedom Radio ta yi da babban mai taimakawa gwamna kan harkokin mutane masu bukata ta musamman Tasi’u Shehu Garko ya ce, ‘yanzu haka mutum tara ne suka hallara a ofishin shugaban ma’aikatar domin karbar takardar kama aikin’.

Ya kuma ce, sauran ragowar mutane masu bukata ta musamman da suka nemi aikin za a tattauna yadda za a basu takaradar kama aikin a nan gaba.

Rahoton: Mukhtar Iliyasu Dumbulun

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!