Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Na bai wa ‘yan jarida damar samun bayanai yayin mulkina- Shugaba Buhari

Published

on

  • Gwamnatina ta yi kokari matuka wajen bai wa ‘yan jarida kariya da ‘yancin samun bayanai.

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma bai wa ‘yan jaridar damammaki duba da rawar da suke takawa wajen isar da sakonni a tsakanin al’umma.

 

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ce, gwamnatinsa ta yi kokari matuka wajen bai wa ‘yan jarida kariya da ‘yancin samun bayanai a zamanin mulkin sa.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar a wani bangare na bikin ranar kare ‘yancin yan jarida da ake gudanarwa Larabar makon nan.

Shugaba Buhari ya kuma ce, ya zama wajibi a yabawa ‘yan jarida duba da yadda suke aiki tukuru wajen sanar da al’ummar kasa al’amuran da suka shafi kasa da ci gabansu.

Rahoton: Madeena Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!