Kaduna
Masu Bukata ta musamman zasu sami kulawa ta musamman wajen rijistan katin zabe – INEC

Masu Bukata ta musamman zasu sami kulawa ta musamman wajen rijistan katin zabe- INEC
Hukumar zabe ta kasa ta ce masu bukata ta musamman, mata masu ciki da tsoffi zasu sami kulawa ta musamman idan suka je yin rijistan katin zabe.
Jami’ar Hulda da jama’a ta hukumar zabe, reshen jihar Kaduna Rukayyatu Sani Imam ce ta bayyana haka lokacin zantawarta Freedom Radio.
Rukayyatu Imam ta ce dokar hukumar zabe ta shekarar 2022 ta yi tanadin baiwa masu bukata ta musamman da mata masu ciki da tsoffi kulawa ta musamman lokacin rijistan katin zabe da kuma lokacin zabe na gama gari.
A cewarta, yanzu haka hukumar ta kammala rijistan mutane sama da 18, 690 a sabon rijistan da aka fara a Kaduna.
“Yanzu haka akwai katin zabe sama da dubu dari na shekarun baya da ba’a karba ba a Kaduna”
Idan za’a iya tunawa hukumar zabe ta fara rijistan katin zaben a ranar 18 ga watan Ogustan shekarar nan ta 2025.
You must be logged in to post a comment Login