Labarai
Masu hakar ma’adanai a kano suna bin barauniyar hanya – Dr Getso
Gwamnatin jihar Kano ta ce masu hakar ma’adanai a Kano na bin barauniyar hanya wajen samun albarkatun kasa.
Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan ta cikin shirin “Duniyar mu a yau” na nan tashar Freedom Redio.
Getso ya ce, masu hakar ma’adanan mafi yawansu basu da ilimin sanin hakar ma’adanan wanda hakan ke haifar musu da illa ga lafiya.
” Cikin ma’adanan kasa akwai dalma, wadda nayi bincike a kanta, kuma binciken ya nuna akwai wata guba a cikin ta da ke shafar kwakwalwar su a farkon rayuwar su ko kuma karshe ba tare da sun sa ni ba”
Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya kuma ce sauran ma’adanan kasar ma kowanne yana da illar ga lafiya musamman ga masu hakar su ba tare da ilimi ba.
“Hakar ma’adanan ba bisa ka’ida ba na daya daga cikin abinda ke haifar da lalcewar muhalli” a cewar Dr Getso.
You must be logged in to post a comment Login