Labarai
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya goyi bayan kara wa ma’aikatan hukumar customs albashi
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana goyon bayan sa kan shirin gwamnatin tarayya na yiwa ma’aikatan hukumar fasakauri ta kasa Kwastam karin albashi domin kara karfafa musu gwiwa.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin biki yaye ma’aikatan hukumar da aka basu horo a Kwalejin horas da jami’an na kwastam da ya gudana jiya Alhamis a birnin tarayya Abuja.
A cewar sa rawar da hukumar ta kwastan ke takawa ta fi gaban a misalta, ciki har da rawar da suke takawa wajen kare dukiyoyin al’umma ta hayar dai-daita zirga-zirgar mutane da kayaki a kan iyakokin kasar da uwa uba tara kudaden haraji.
Mataimakin shugaban kasar ya kuma ya ba da sabon tsarin da hukumar ta fito da shi na yin gwanjon kayayyaki ta hanyar zamani da take yin amfani da yanar gizo, inda ya ce shakka babu hukumar ta kwastam na taka muhimmiyar rawa wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.
Tun da fari da yake nasa jawabin shugaban hukumar ta kwastam Kanal Hamid Ali mai ritaya ya ce cikin watan Mayun da ya gabata hukumar ta tara harajin da yafi kowanne tsoka da ya kai naira biliyan dari cikin wata daya kacal.
Ya kuma ce an fara karatu a Kwalejin horas da ma’aikatan hukumar ne a watan Janairun wannan shekara inda aka yaye manya ofisoshi 40 bayan an basu horo na watanni shida.