Kaduna
Matasa sun kashe yan bindiga 6 a Sokoto.

Matasan karamar hukumar Shagari da ke a jahar Sokoto sun kashe wasu ‘yan bindiga shidda da ake zargin suna cikin wadanda suka addabi yankin.
Shugaban karamar hukumar Alhaji Muhammad Maidawa ya ce da safiyar Alhamis din da ta gabata ne, labari ya zo masa akwai wasu bakin Fulani da aka afkawa a garin na Shagari. Yace amma komai ya lafa sojoji sun kwantar da tarzomar.
You must be logged in to post a comment Login