Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Matashi ya hallaka kansa saboda an kawo kudin auren budurwarsa a Kano

Published

on

Wannan matashi mai suna Ashir Musa Sani ‘dan shekara 22 ya hallaka kansa ta hanyar cakawa kansa wuka, a unguwar Dan Rimi dake karamar hukumar Ungogo.

Mahaifin matashin mai suna Musa Sani ya ce ana zargin ‘dan nasa ya hallaka kansa ne bayan da ya samu labarin cewar an kawo kudin auren budurwar da yake so.

Marigayin Ashir Musa jami’an sunturi ne a unguwar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce, matashin ya rasa ransa ne bayan da ‘yan uwansa suka kai shi asibiti sanadiyyar galabaitar da yayi bayan da ya cakawa kansa wuka.

Yanzu haka dai, tuni aka yi jana’izar sa, kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!