Labarai
Matsalar fyade : Ina goyan bayan hukuncin dandaka ga masu fyade – Sarkin Karaye
Sarkin Karaye Alhaji Dr, Ibrahim Abubakar na II ya bayyana goyan bayan shi kan hukuncin yin dandaka ga duk wanda aka kama da laifin yin fyade.
Sarkin na Karaye ya bayyana goyan bayan sa ya yin da yake tarbar kwamishiniyar kula da al’amuran mata ta jihar Kano Dr, Zahra’u Muhammad Umar a fadar sa bayan da ta kai masa ziyara.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da jami’in yada labarai na masarautar Haruna Gunduwawa ya fitar cewa Sarkin na Karaye na cewa daukar wannan matakin kan masu aikata wannan laifin zai zama izina ga wadanda ke aikata fyade a kasar nan.
A dai ranar 15 ga watan Yulin da ya gabata ne majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da dokar yin Dan-daka ga wadanda aka kama da aikata fyade a jihar Kano, ya yin da majalisar malamai ta Kano taki amincewa da dokar kan cewa hukuncin yin dandaka ka masu yin fyade ya sabawa koyar addinin musulunci.
Bugu da kari batun yi wadanda suke aikita fyade Dandaka ya jawo kace-nace a tsakanin al’umma tun bayan da wasu gwamnoni suka amince da daukar wannan matakin.
You must be logged in to post a comment Login