Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

El-rufa’i ya sanya hannu kan dokar dandaka ga masu fyade

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya sanya hannu kan dokar da aka yi wa kwaskwarima ta hukunta masu aikata laifin fyade musamman ma ga kananan yara.
Hukuncin dai ya hadar da yin dandaka da kuma hukuncin kisa ga duk namijin da aka kama da laifin yin fyaden.
A ranar larabar makon jiya ne dai majalisar dokokin Jihar ta amince da gyaran dokar, sannan aka aikewa gwamnan domin sanya hannu a kai.
Ko a ranar alhamis din da ta gabata mun kawo muku tattaunawa da kwamishiniyar mata ta Jihar Kaduna Hajiya Hafsat Baba, tana mai cewar dama can a shirye gwamnan yake domin sahalewa dokar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!