Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Matsalar hanya: Ƴan majalisun Kano sun farga

Published

on

A zaman majalisar dokokin jihar Kano na yau shida ga watan October ƴan majalisun sun mayar da hankali wajen nemawa yankunansu hanyoyi duba dacewa matsalar hanya ta yiwa yankunan karkara yawa ga kuma yanayi na damina al’umma na shan wahala wajen zirga-zirgar yau da kullum.

Ƴan majalisun da suka gabatar da ƙudirin neman gyaran hanyoyin sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar Kumbotso Mudassir Ibrahim Zawachiki da Yusuf Sulaiman Baban Gida mai wakiltar Gwale sai Ɗan majalisa mai wakiltar Bunkure Mahmud Uba Gwurjiya dana Ɗanbatta Murtala Musa Kore sai na Shanono da Ɓagwai Ali Ibrahim Isah Shanono sai na Gwarzo Inusa Haruna Kayyu.

Wakiliyar mu Khadija Ishaq Muhammad ta rawaito cewa cewa ƴan majalisun sun nemi gwamnatin Kano da ta duba al’ummar yankunansu ta magance musu matsalolin lalacewar hanyoyin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!