Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Matsalar idanu: Za mu samar da makarantar ƙwawararru a fannin –Kwamishinan Lafiya

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana dab da buɗe makarantar ƙwararru masu jinyar ido a jihar.

Kwamishin lafiya na jihar Dakta Aminu Ibrahim tsanyawa ne ya bayyana hakan, a taron kungiyar ƙwararru ma su jinyar ido ta ƙasa reshen jihar Kano.

Ya ce “Sakamakon yadda mutanen jihar Kano ke tafiya kudancin ƙasar nan domin neman ƙwarewa a fannin kula da lafiyar ido, a yanzu mun ga dacewa samar da makarantar a nan Kano”.

“mun kuma lura cewa ana samun yawaitar masu fama da lalurar ido, kuma mafi yawa suna shan wahala kafin su samu kulawar da ta da ce, amma samar da makarantar zai taimaka wajen inganta lafiyar al’umma”.

Taron dai an gudanar da shi a gidan gwamnatin jihar Kanoa a ranar Talata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!