Labarai
Matsin rayuwa: DSS ta hana NLC yin zanga-zanga
Hukumar tsaron farin kaya DSS ta yi kira ga ƙungiyar ƙwadago NLC da ta janye ƙudurinta na shirya zanga-zangar gama gari domin samun zaman lafiya a Najeriya.
Ƙungiyar NLC ta sanar da fara yajin aikin a ranar 27 da 28 ga watan Fabarairu domin nuna rashin jin daɗinta kan halin matsin rayuwa da al’umma ke ciki a ƴan Najeriya.
Wannan na zuwa ne yayin da kwamishinan ƴan sanda a Abuja Ben Igweh cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar, yana mai cewa rundunarsa ba ta da masaniya kan zanga-zangar da ake shirin yi a Abuja.
Sanarwar ta DSS ɗauke da sa hannun Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Dakta Peter Afunanya, ta ce DSS ta samu labarin akwai wasu mutane da ke shirin yin amfani da zanga-zangar wajen tayar da husuma da kuma rikici.
DSS ta kuma yi kira ga ƙungiyoyin su tattauna a maimakon yin abin da ka iya tayar da hankali.
You must be logged in to post a comment Login