Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Maulid: An buƙaci al’umma suyi koyi da irin ɗabi’un Manzon Allah SWA

Published

on

An buƙaci al’umma da suyi koyi da ɗabi’un ma’aiki SAW da sahabban sa domin samin dacewa anan duniya da kuma gobe kiyama

Malan Ibrahim Khalil ne ya bayyana hakan a yau Asabar yayin taron maulidin fiyayyen halitta da zuri’ar tsohon Alƙalin Alƙalai Alhaji Bashir Ahmad suka shiya domin gabatar da muƙaloli kan yadda za’a ƙara faɗakar da al’umma yin koyi da ɗabi’un sa ma’aiki SAW

Malan Ibrahim Khalil ya ce matuƙar mutane zasu dunga irin wannan tunatarwa ga al’umma tom wannan zai ƙara sanya soyayyar ma’aiki a cikin al’umma

Shima da yayi jawabi Sheikh Tijjani Bala Ƙalarawi cewa yayi matuƙar al’umma na neman tsira a rayuwa to ya zama wajibi su ɗauki halayyar ma’aiki da Sahabbai

Haka kuma ya shawarci al’umma da su kasance masu kyautatawa al’umma musamman marasa ƙarfi da dukkan nau’i na abinci da sauran kayan anfanin yau da kullum domin neman tsira

Da yake jawabi jagorar Shirya Maulidin kuma Babban Ɗa ga Tsohon Alƙalin Alƙalai Alhaji Naziru Bashir Ahmad Ya ce sun shirya wannan Maulidi ne ƙara tunawa da shagayowar watan haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW

Adan haka yasa suka shirya domin gayyato malamai da sauran al’ummar gari domin a tunatar da al’umma kan girma da Annabin tsira yake da shi da kuma koyi da halayansa kyawawa

Naziru ya kuma ce wannan Maulidi suna gudanar da shi a duk shekara inda suke gayyatar al’umma domin azo aci asha domin tunawa da wannan watan mai matukar muhimmanci ga dukkan Musulmin duniya

Daga karshe anyiwa ƙasar nan addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai anfani da kuma yin addu’a ga iyalan tsohon Alƙalin Alƙalai Alhaji Bashir Ahmad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!