Connect with us

Nishadi

Mawaƙa na kan gaba wajen haifar da koma baya a ƙasar nan – Busayo Oshakuade

Published

on

Mawaƙin gambarar zamani Busayo Oshakuade ya zargi ƴan’uwansa mawaƙa da yaɗa saƙonin da bai kamata ba, musamman ma wajen aibata ƙasar nan.

Fitaccen mawakin gambarar zamani a masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood mazaunin ƙasar waje mai suna Busayo Oshakuade ya yi kira ga ƴan uwansa mawaƙa da su gujewa nuna tunƙaho da taƙama.

Har ma ya buƙace su da kauracewa yaɗa abubuwan da ba gaskiya ba musamman wanda za su haska wani abu wanda za’a ga aibun Nigeria.

Mawaki Busayo ya ce, za’a iya samun ci gaba a ƙasar nan, in har waɗanda suke cikin masana’antun Nishaɗi za su yi abinda ya dace wajen isar da saƙonnin su.

Haka kuma, ya ƙara da cewa akwai wasu sinadarai da waƙoƙi suke da su, wanda ya ke kawo sauye-sauye da dama a cikin al’umma.

Tare da basu shawara kan su haɗa kawunan su da ƙungiyoyinsu na mawaƙa na cikin gida da masu tasowa har ma da na ƙasashen waje.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!