Labaran Kano
Maza sunfi bada muhimmanci ga sunnar karin aure –Halima Shitu
Tsohuwar mataimakiyar babban kwamandan Hisbah na jihar Kano, kuma shugabar kungiyar mata musulmi ta Africa wato (AMWA) Malama Halima Shitu Abdulwahab ta bayyana cewa babu wata Sunnah da maza sukafi baiwa muhimmanci face sunnar kara Aure.
Malamar tayi wannan jawabi ne a yayin taron da mai dakin Sarkin Kano Hajiya Maryam Muhammad Sanusi II ta shirya a fadar sarki wanda aka yi a you don dakile rikicin cikin gida tsakanin iyali a Arewancin kasar nan.
Malam Halima shitu ta kara da cewa mace tana da daraja tana da kimar da har Allah madaukakin sarki ya yi mata, a saboda haka ya sanyawa sura guda sunan Maace wato Suratul Nisa’i.
Har ila yau malamar ta Kara da cewar, da za’a tara mata ‘yan uwa to tabbas zata yi musu wa’azi akan irin hakkokin da Allah ya dora musu na matayen su, sai dai abun takaicin shi ne basa maida hankali akan su, illa kawai kan batun karin Aure.
Wakiliyar mu Samira Sa’ad Zakirai ta rawaito cewa malamar na ambato muhimman batutuwa da ya kamata namiji ya yi wajen sauke nauyin da rataya a wuyan sa da suka hada da nemowa matarsa abinci da sha da kuma sutura ya kuma bata cikakkiyar kulawa, wannan itace cikakkiyar sunnar manzon Allah SAW.
Rubutu masu alaka:
Tilas a magance cin zarafin mata- Mai dakin Sarkin Kano.
Za’a koyar da fursunoni arba’in karatun Firamare
Kano na da daliban sakandire fiye da dubu dari bakwai (700,000)