Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Mata da miji sun sha duka a hannun wanda ake zargi da kwartanci

Published

on

Mata da miji sun sha duka a hannun wanda ake zargi da kwartanci

Wani magidanci mai suna Mallam Bello da matarsa sun gamu da ibtila’I inda wani mutum mai suna Sulaiman Saleh ya yanke su da wuka a wuya da kuma hannayen su da ma wasu sassan jiki na matar.

Al’amarin ya faru ne a daren Litinin din nan a kauyen Wutar Kara da ke karamar hukumar Rano a nan Kano.

Ana zargin Sulaiman ya kutsa kai cikin gidan magidancin tare da yunkurin zakkewa mai dakin sa, sai dai ya samu tasgaro, domin kuwa ta kwarma masa ihu, wanda hakan ya sanya mijinta Mallam Bello ya kawo mata dauki.

Sai dai wanda ake zargin yayi amfani da wukar dake tare dashi inda ya yanki magidancin a wuya da hannayen sa, sannan ya yanki matar a wuya da sassan jikin ta.

Rubutu masu nasaba:

Rundunar Yan sanda ta damke wata mace da ake zargin ta sa wa mijinta shinkafar bera a abinci

Maza sunfi bada muhimmanci ga sunnar karin aure –Halima Shitu

Freedom Radio ta samu tattaunawa da magidancin yayin da yake karbar kulawa a gadon asibiti inda ya bayyana takaicinsa kan faruwar hakan.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya ce sun samu labari kuma al’ummar unguwar sun kaiwa iyalin dauki har ta kai sun lakadawa wanda ake zargin duka har ya galabaita.

Izuwa yanzu dai ‘yan sanda sun dawo da wanda ake zargin zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed dake nan Kano domin cigaba da jinyarsa, yayin da ‘yan sanda ke cigaba da bincike akai.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!