Labarai
Mazauna Dawakin Kudu sun nemi daukin Gwamnatin Kano

Mazauna Karamar hukumar Dawakin Kudu a Kano, sun bukaci gwamnatin jihar da ta kai musu dauki kan abin da suka kira dauki daidai da wasu bata gari ke yi musu.
A cewar mazauna yankin, wasu bata gari da ba a kai ga gano su ba, su na cin karensu babu babbaka a kan hanyar Mariri zuwa garin Dawakin Kudu inda har ta kai ga suna yin kisa da kuma fashi da makami a kan hanyar.
A zantawar Freedom da wani mazaunin yankin Dakta Muhammad Tahir Abdullahi, ya yi karin haske kan wannan lamari.
Latsa alamar Play da ke kasa domin sauraron muryarsa.
Al’ummar wannan yanki dai sun bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gaggauta daukar matakir mataki a yankin.
You must be logged in to post a comment Login