Labarai
Me ya sa Gwamnatin Kano ta dage lokacin komawa Makaranta?
A Asabar din da ta gabata ne Kwamishinan Ilimi na Kano Malam Umar Haruna Doguwa ya sanar da dage komawa makarantun Firamare da Sakandire har zuwa nan gaba.
Sai dai bai bayyana dalilan daukar wannan mataki ba.
Me iyayen yara ke cewa?
Wasu iyaye da Freedom Radio ta zanta da su sun ce ba su ji dadin sanarwar ba kuma ta sanya musu fargaba domin rashin sanin takamaiman dalilin, inda wasu ke fargabar ko matsalar tsaro ce.
Wasu kuma iyayen sun ce, dage komawa makarantar ya zo musu a daidai domin za su sake samun damar sake kintsawa.
Me yasa Gwamnatin ta dage komawar?
Wata majiya mai tushe a ma’aikatar ilimi ta Kano ta tseguntawa Freedom Radio cewa babban dalilin dage hutun shi ne rashin shiryawa shirin ciyar da dalibai abincin ‘Tatsotse’ da rashin kammala dinka kayan makarantar dalibai, wanda Gwamnatin ta ke son dalibai su koma da su.
Labarai masu alaƙa:
Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da dokar ta-baci a fannin ilimi
Gwamnatin Kano za ta haɗa gwiwa da Ghana don farfaɗo da ilimi
Domin jin gaskiyar wannan batu Freedom Radio ta yi ta neman wayar Kwamishinnan Ilimi na Kano Malam Umar Haruna Doguwa tun ranar Asabar amma wayarsa ba ta shiga.
Sakamakon hakan Freedom Radio ta tura wakilinta zuwa ma’aikatar ilimi ta Kano inda ya samu zarafin ganawa da Kwamishinan amma ƙememe ya ƙi yarda ya yi masa cikakken bayani, sannan ya ƙi amincewa a naɗi muryarsa.
Abin da Doguwan ke jaddadawa shi ne “Wallahi ba wani abu, lafiya ƙalau, kuma ba gazawar Gwamnati a ciki, sai inganta lafiyar dalibai” ya maimaita wannan sama da sau uku.
You must be logged in to post a comment Login