Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Menene makomar ‘Yan Mari bayan da gwamnati ta soke ayyukan su.

Published

on

A Litinin ne gwamnatin Kano ta sanar da cewar an soke dukkanni ayyukan Makrantun Mari a jihar Kano, ta hannun shugaban kwamitin sake yin nazari kan karatun Almajiranci da na Tsangayu.

Wasu daga cikin malaman makarantun ‘yan Marin sun ce a gaskiya wannan matakin yayi tsauri kuma yaran za su shiga cikin wani hali.

Malaman da suka nemi a saka sunan su, sun ce matakin zai sanya ana kama kangararrun yaran a kais u gidajen yari maimakon a kais u Makarantun ‘yan Mari ko na tsangaya.

A dai jiya Litinin ne biyo bayan karbar rahoton da kwamitin kwararru na sake duba yanayin karantun  Almajirai a jihar Kano wanda  Muhammad Tahar Adamu yake jagoranta  gwamnatin Kano ta bada umarnin soke makarantun ‘Yan Mari.

A cewar Muhammad Tahar Adamu “Baba Impossible” gwamnatin Jihar Kano ta soke ayyukan gudanar da duk wani gidan Mari a nan Kano, saboda irin ayyukan da suke gudanarwa.

Shugaban Kwamitin sake fasalta tsarinAlmajiranci a nan Kano Dr Muhanmad Tahar Adam ne ya sanar da hakan a yau lokacin da da ya jagoranci zagayen ziyarar gani da ido da jami’an hukumarsa ke gudanarwa a nan Kano, don tantance yadda ake gudanar da gidajen  ‘Yan Marin suke.

Kazalika, Dr Muhammad Tahar Adam ya yi karin bayani kan cewa matakin bai shafi   Makarantun Islamiyya da na Allo ba.

Har ila yau, kwamitin yace ya gano cewar ana take hakkin yara a wasu daga cikin irin wadannan makarantu na ‘Yan Mari.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!