Labaran Wasanni
Messi ya yi kunne doki da Mascherano a yawan wasanni ga Argentina
Dan wasan kasar Argentina Lionel Messi, ya yi kunne doki da Javier Mascherano wajen yawan wasanni ga kasar sa, a wasan da tawagar Argentina ta samu galaba akan kasar Paraguay da ci daya mai ban haushi.
Shi dai Javier Mascherano ya bugawa kasar ta Argentina wasanni 147 a tarihin da Messi ya karya a fafatawa da kasar ta yi da Paraguay a gasar Copa America ta 2021.
Mascherano ya taya babban dan wasan Messi murna ta kafofin sada zumunta.
Idan har mai horarwa Luis Scaloni zai baiwa Messi damar fara wasa a mako mai zuwa a kan Bolivia, to zai zama dan wasan da ya fi kowa taka leda a kasar ta Argentina, fiye da irin su Javier Zanetti da Diego Maradona.
A yanzu dai kasar ta Argentina ta samu nasarar tsallakawa zagayen daf da na kusa da na karshe.
You must be logged in to post a comment Login