Labaran Wasanni
Messi zai bar Barcelona
Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Lionel Messi, ya ce zai bar kungiyar a kakar wasanni ta bana bayan kwashe kusan tsawon shekarun 20 a kungiyar.
Kungiyar kwallon kafar ta Barcelona ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa data fitar ga manema labarai dake cewa dan wasan Messi dan asalin kasar Argentina ya mika dukkan wasu takardu dake nuna bukatar tasa ta san barin kungiyar.
Bayyana hakan ga dan wasan na Bacerlona Messi, ya biyo bayan rashin nasarar da kungiyar ta yi kwanaki 11 a hannun kungiuyar kwallon kafa ta Bayer Munich a gasar cin kofin zakarun turai ta Champion League wasan na kusa da karshe da ci 8-2.
Rashin nasarar da kungiyar ta yi da ci 8-2 ita ce rashin nasara a kan dan wasan Messi mafi muni a tarihin wasannin sa.
Haka zalika tsawon shekaru 59 rabon da kungiyar ta Barcelona ta fuskanci irin wannan rashin nasara a tarihin ta.
Messi dai ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Duniya sau shida a kungiyar tasa ta Bacerlona, ya kuma taimakawa kungiyar ta Bacerlona wajen lashe kofin Laliga kasar ta Spaniya 10 da kofin zakarun turai Champion League 4.
Rabon da kungiyar ta Bacerlona ta yi rashin nasarar daukan kofi a kakar wasanni tun daga shekarar 2007/2008 sai a bana.
You must be logged in to post a comment Login