Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mikel Arteta ka iya rasa aikin sa idan Arsenal ta yi rashin nasara a wasanni uku masu zuwa

Published

on

Mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta, zai iya rasa aikin sa na horas da kungiyar, matukar tawagar bata yi nasara a wasanni uku da za ta buga nan gaba, a gasar premier kasar Ingila ba.

Arsenal dai za ta fafata wasan ta na gaba da Manchester City a ranar 28 ga watan da muke ciki na Agusta inda a ranar 11 ga watan Satumba za ta yi da Norwich City sai kuma a ranar 18 ga satumbar ta yi da Burnley

Tawagar ta Arsenal “tana mawuyacin halin da ba ta taba shiga makamancin sa ba bayan da ta fara kakar Premier League ta bana ba da karsashi ba”  inji Mikel Arteta.

Kungiyar dai ta yi rashin nasara da ci 2-0 a gidan Brentford a wasan farko da ta yi kana ta  sake rashin galaba a hannun Chelsea itama da ci 2-0 a karawar mako na biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!