Labarai
Miliyoyin mutanen Jihohin Kano da Jigawa na fama da kagin talauci – Buhari
Kwamitin shugaban kasa da ke kula da harkokin tattalin arzikin kasa, ya ce, akalla mutane miliyan 12 na fama da kangin talauci a jihohin Kano da Jigawa.
Mataimakin shugaban kwamitin kula da tattalin arzikin na kasa, Dr. Muhammmad Sagagi ne ya bayyana hakan yayin taron karshen shekara da kungiyar tsofaffin daliban kwalejin nazarin harkokin mulki reshen jihohin Kano da Jigawa ta gudanar jiya anan Kano.
Ya ce, samar da aikin yi ga jama’a lamari ne da kowane dan kasa ke da alhaki akai, domin kuwa gwamnati ita kadai, ba za ta iya sanarwar kowa da kowa aiki ba.
Ana sa jawabin shugaban kungiyar Dr Muhammad Sabi’u Umar ya ce, lamarin rashin aikin yi da talauci da ya yi katutu tsakanin matasa musammam a arewacin kasar nan abune da ya kamata gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su mai da hankali akai.
Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa, kungiyar za ta kuma bai wa gidajen marayu da masu rangwamin gata har ma da gidajen gyaran hali dake nan Kano tallafi.
You must be logged in to post a comment Login