Labarai
Minista: Zamu Haɗa hannu da KACCIMA domin bunƙasa kasuwanci
Gwamnatin tarayya ta ce, za ta cigaba da aiki kafada da kafada da Cibiyar Kasuwanci ma’adanai masana’antu da zuba jari ta jihar Kano KACCIMA, domin kara habbaka harkokin Kasuwanci.
Karamin Ministan ma’aikatar harkokin ma’adanai Dakta Uchechukwu Sampson Ogah, ne ya bayyana hakan yau Alhamis a nan Kano yayin da ya kai ziyara ofishin cibiyar.
Dakta Uchechukwu Sampson Ogah, ya ce, ya kawo ziyarar aiki ne a nan Kano, don haka ya ziyarci cibiyar domin kara karfafa alaka kasancewar su manyan ‘yan kasuwa don kara bunkasa cinikayya.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban kungiyar ta KACCIMA, Ambasada Usman Darma, cewa ya yi ministan ya zo Kano ne domin duba wurin da gwamnatin tarayya za ta gina cibiyar sarrafawa tare da sayar da gwala-gwalai a nan Kano, amma suna ganin wurin bai can-canci yin aikin ba.
Ya kara da cewa kasancewar gwal kadarar da za a iya daukar na miliyoyin Naira a cikin aljihu a yi yawo da shi ba tare da wani ya san menene ba, ya kamata a samar da wurin sarrafa shi ya kasance a yanki mai tsaro.
Cibiyar ta KACCIMA, ta bukaci gwamnati da ta yi la’akari da bukatar tsaro a harkar gwala-gwalai ta fuskar karkato da aikin zuwa kasuwar baje-koli domin samun ingantacce tsaro tare da kyakkyawan yanayin aikin.
You must be logged in to post a comment Login