Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Ministan birnin tarayya ya hana sallar idi a masallacin idi sai dai ayi a masallatan juma’a

Published

on

Ministan birnin tarayya Abuja Muhammad Bello ya ba da umarnin haramta yin sallar idi a babban masallacin idi da ke titin Umaru Yar’adua  da ke birnin sai dai a gudanar da sallar ta bana a masallatan juma’a.

 

Ya ce daukar matakin ya biyo bayan shawara da jami’an lafiya na birnin su ka bayar don rage cakuduwan jama’a wanda hakan wani mataki ne na kare kai daga yaduwar cutar corona

 

Muhammad Bello ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke ganawa da wata tawagar limamai karkashin jagorancin Imam Tajudeen Adigun wadanda suka kai masa ziyara ofishinsa

 

 

Ministan ya kuma shawarci limaman da su gudanar da sallar idi a masallatansu na juma’a

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!