Labarai
Ministan kwadago ya gaza, don haka ya sauka daga mukamin sa – NARD
Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa NARD ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da ministan kwadago da samar da aikin yi Chris Nigige ko kuma ya sauka daga mukamin sa.
Shugaban kungiyar Dr Uyilawa Okhuaihesuyi ne ya bayyana hakan, biyo bayan kalaman da ministan kwadagon ya yi ta kafar talabijin ta kasa NTA, da ke bayyana cewa basu shirya zama da kungiyar ba.
Dr Uyilawa ya ce, ministan ya gaza shawo kan matsalolin da suke fuskanta, wanda ya tilasata su tsunduma yajin aiki, wannan ya nuna cewa ba zai iya ci gaba da jagorantar mukamin da yake kai ba.
Kungiyar ta kuma bukaci ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire da ministan kwadagon Chris Ngige, da kuma shugaban kungiyar kwararrun likitocin hakori ta kasa Dr Tajudeen Sanusi, da su sauka daga mukaman su domin kuwa sun gaza.
Wannan dai ya biyo bayan yajin aikin da kungiyar ke yi tsawon mako guda, biyo bayan zargin da kungiyar ta ken a kin cika alkawuran da gwamnatin tarayya ta yi musu.
You must be logged in to post a comment Login