Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari ya sauka daga kan mukamin sa kan karin fetur da wuta – NANS

Published

on

Kungiyar dalibai ta kasa shiyya ta hudu (NANS) ta bukaci shugaba Buhari ya sauka daga mukamin sa sakamakon yadda aka samu Karin farashin man fetir a baya bayan nan ba.

Babban jami’in kungiyar Kowe Odunayo Amos ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar.

Sanarwar ta ce wannan kari ba komai yake nufi ba sai kara matsantawa yan kasar nan don kuwa a halin yanzu al’umma na cikin halin matsin rayuwa sakamakon yadda annobar corona ta illata tattalin arziki.

Sanarwar ta bukaci shugaba Buhari da sauran mataimakan sa da su sake duba kan Karin man fetur din, ko kuma su sauka daga makaman su.

Ta cikin sanarwar dai kungiyar ta ce Karin farashin zai zamo matsawa ga al’ummar kasa musamman yadda bangaren wutar lantarki suma suka kara farashin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!