Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Monguno: Muna daf da kawo karshen rashin tsaro a Najeriya

Published

on

Fadar shugaban kasa ta sha alwashin yin duk me yiwuwa wajen ganin ta kawo karshen rashin tsaro da ke addabar sassa daban-daban Najeriya nan ba da jimawa ba.

 

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro manjo janar Babagana Monguno mai ritaya ne ya bayyana haka bayan kammala wani taro kan harkokin tsaro da shugaban kasa ya yi jiya a fadar asorok.

 

A cikin wata sanarwa da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron ta fitar, ta ce, an dage ci gaba da tattaunawa da shugaban kasar ya fara a jiya da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaron zuwa ranar talata na makon gobe don ci gaba da neman hanyoyin da za abi don magance matsalolin da ke addabar Najeriya.

 

Ya ce, bako shakka gwamnati ta damu matuka game da halin da ake ciki kuma tana ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki da nufin lalubo hanyoyin da za a dakile matsalar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!