Labarai
Mu dage da addu’a a yayin bikin sallah – Jarman Matasan Arewa
Sponsored
Fitaccen ‘dan gwagwarmayar nan Ambasada Yusuf Hamza Jarman Matasan Arewa, ya nemi al’ummar musulmai musamman matasa da suyi amfani da lokacin bukukuwan sallah wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya.
Ambasada Yusuf Hamza ya yi wannan kira ne ta cikin wata sanarwar sakon barka da sallah ga al’umma da ya fitar.
Sanarwar ta nemi al’ummar musulmai da su kaucewa amfani da wadannan lokuta wurin aikata alfasha da sunan bikin sallah.
“Mu na kira ga gwamnati da ta samar da wasu tsare-tsare da za su bunkasa rayuwar matasa, domin su ne manyan gobe” a cewarsa.
A karshe ya kara jaddada kiran al’umma kansu kara zage dantse wajen yin addu’o’I musamman a wannan wata mai albarka, domin magance matsalolin da ke addabar al’umma.
Ambassada Yusuf Hamza dai daya ne daga cikin jagororin matasan Arewa wadanda ke kan gaba wajen fafutukar inganta rayuwar matasan.
You must be logged in to post a comment Login