Labarai
Muna goyon bayan gina titin jirgin ƙasa a Kano – Ƙungiya
Ƙungiyar tabbatar da aminci da kyautata ayyuka a jihar Kano ta goyi bayan gwamnatin Kano a kan yunƙurin ta na samar da titin jirgin ƙasa.
Bayanin hakan ya fito ne ta cikin sanarwar bayan taro mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Farfesa Abdu Salihi da sakataren ƙungiyar Dr. Garba Shehu bayan kammala wani taro na yin guda da ƙungiyar ta shirya wa ƙwararru wanda aka tattauna game da aikin titin jirgin.
Sanarwar ta nuna cewa yunƙurin da gwamnatin Kano ta yi na wannan aiki abu ne mai kyau da zai taimaka wa harkokin sufuri, wanda bai kamata a ce an bar Kano a baya ba wajen ayyukan ci gaba.
Haka kuma yayin da yake zantawa da manema labarai game da taron Farfesa Salihi ya ce, sun shirya taron ne domin fahimtar amfanin al’amarin da kuma duba ribar da aikin zai haifar ga al’ummar Kano tare da duba yiwuwar gwamnatin ta ci gaba ko akasin haka.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa sanarwar ta shawarci gwamnatin Kano da ta yi amfani da tsarin haɗin gwiwa da ƴan kasuwa masu zaman kan su yayin gudanar da aikin sannan ƙungiyar ta yabawa gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje akan tsayawa wajen tabbatar da aikin tare da kira ga mutane da su daina sanya siyasa a kan yunƙurin ayyukan ci gaban jiha da ake gudanarwa.
You must be logged in to post a comment Login