Labaran Wasanni
Muhammad Salah ya zura kwallo 100 a premier din kasar Ingila
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohamed Salah ya zura kwallo ta 100 a gasar premier din kasar Ingila cikin wasanni 162 da ya buga.
Salah ya zura kwallon ne a wasan da kungiyar sa ta Liverpool ta doke Leeds United da ci 3-0 a gasar ta premier a yau Lahadi 12 ga Satumbar shekarar 2021.
Ƙungiyar Liverpool ta ɗauki ɗan wasan RB Leipzig Ibrahima Konate
Liverpool ta ziyarci Leeds United a wasan mako na 4, inda Salah ya fara zura kwallo a minti na 20 da fara wasan.
Kwallon da Salah ya ci ita ce ta 100 da ya zura a raga a gasar Premier, kuma ta 5 da ya yi wannan bajintar a karancin wasanni, bayan Alan Shearer a wasa na 124, sai Harry Kane a karawa ta 141 da kuma Sergio Aguero a fafatawa ta 147.
Na 4 a irin wannan kokarin shine Thierry Henry da ya ci kwallo ta 100 a gasar Premier a wasa na 160, sai Salah wanda ya ci a karawa ta 162.
You must be logged in to post a comment Login