Connect with us

Labarai

Mun ɗauki matakan samar da wadatatciyar wutar lantarki- Kashim Shettima

Published

on

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Gwamnatin Tarayya na ƙara ɗaukar matakai domin samar da wadatatciyar wutar lantarki a faɗin Najeriya.

 

Kashim Shettima, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin ƙaddamar da sabuwar hedikwatar Hukumar Kula da Bashin Wutar Lantarki ta Najeriya, wato Nigerian Electricity Liability Management Company, a birnin Abuja.

 

Ya kuma umarci hukumar da ta ƙara ƙaimi tare da taka rawar gani wajen warware matsalolin da ke addabar ɓangaren wutar lantarki, domin samun ingantaccen haske ga al’umma.

 

Mataimakin shugaban kasan, ya jaddada cewa gyare-gyaren da gwamnati ke aiwatarwa za su taimaka wajen ƙara samar da wuta tare da rage matsalolin da masu amfani da ita ke fuskanta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!