Labarai
Mun amince da kudurin kwarya-kwaryar kasafin kudin bana – Ahmad Lawal

Kudurin kwarya-kwaryar kasafin kudin bana da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar dattijai ya shiga karatu na biyu a Larabar nan.
Shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ne ya mika bukatar ga kwamitin kudi na majalisar, sannan ya bukaci kwamitin ya gabatar da rahotonsa ga majalisar a ranar talata mai zuwa don tantancewa.
A ranar talata ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar kwarya-kwaryar kasafin na sama da naira biliyan 842, don neman amincewar majalisar.
You must be logged in to post a comment Login