Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Makaho ya lashewa Kano Lambar Zinare a gasar Para Games

Published

on

Acigaba da gudanar da gasar masu buƙata ta musamman ta ƙasa (National Para Games ) a birnin tarayya Abuja, ‘yan wasan jihar Kano na cigaba da taka rawar gani wajen lashe Lambobi na nasara a gasar.

Daga cikin nasarorin har da ta Dattijo mai shekara 71 , mai lalurar makanta (Blind ), Yahaya Usman da ya samu zama zakara a wasan kurme (Tseren Ruwa na Swimming), na wasan Mita 100.

Ya yin da ɗan wasa Sulaiman Taiwo ya lashe gasar tseren mita 100 a lambar Zinare , sai Fausat Savage data samu lambar Tagulla a jifa mai nisa na Dalma (Shortput).

Ɗan wasan tseren mita 100 , Micheal Olushola, ya lashe lambobin Zinare da Azurfa , a wasan Tennis sai Abiodun Ayodeye da ya lashe lambar Zinare a wasan..

A bangare ɗaya ‘yar wasa Shakirat Abolaji ta lashe lambar azurfa guda biyu a wasan motsa jiki sai ɗan wasaLawanson Sheriff da ya ɗau Azurfa, shima a wasan motsa jiki na Para Athletic.

Ajayi Stephen mai wasan motsa jiki na Para Athletic ya samu nasarar ɗaukar Tagulla a cikin nasarorin da jihar Kano ke cigaba da samu a gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!