Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun bankaɗo Azzaluman da ke damfarar mutane Filayensu- Barista Muhyi

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC, ta sha alwashin yin yaki da masu aikata dabi’un cin hanci da rashawa har ma da masu damfara da cutar mutane filayensu.

Shugaban hukumar Barista Muhyi Magaji Rimingado, ne ya bayyana hakan a yau Talata yayin wani taron wayar da kan matasa kan yadda za su bada gudunmawa wajen dakile matsalar cin hanci da rashawa tare da raba kayan karatu ga ɗalibai tare da karrama wasu mutane takwas da ke bayar da gudunmawa wajen yaki da ɗabi’ar cin hanci da rashawa.

Barista Muhuyi Magaji, ya ce, a shekara nan da muke ciki ta 2024, hukumar ta gano yadda wasu mutane ke shirya yadda suke zaluntar wasu ya hanyar cinye musu filaye.

Haka kuma, yayin taron, Barista Muhyi Magaji Rimingado, ya raba jakunkuna da litattafai da kuma kayar rubutu ga ɗalibai 150, inda ya bayyana cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya umarce shi da ya yi wannan rabo a ci gaba da bikin ranar yaƙi da cin hanci da rashawa na bana.

Da ya ke bayyana farin cikinsa bisa karrama shi da hukumar ta yi, wani matashi Auwal Ahmad Dan-koɗe da hukumar ta karrama bayan da ya tsinci kudi dalar Amurka dubu goma yayin da ya ke yin sharar jirgin sama a nan Kano, ya bayyana jin dadi sa kamar haka.u

Mutane takwas da hukumar ta karrama a yau sun hada da Alkalin Alkali ta Kano Mai shari’a Dije Abdu Aboki da shugaban hukumar tace Finafinai ta Kano Abba El-Mustapha da wasu manyan jami’an Yan sanda biyo da sauransu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!