Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun buɗe shafin N-Power karo na 3 – Ministar jin ƙai

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ɗaddamar da shirin N-power rukuni na 3 zubin farko na mutane dubu biyar da goma a fadin ƙasar nan.

Ministar jin ƙai da kare abkuwar ibtila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana hakan, a wajen ƙaddamar da shirin a Abuja.

Ministar ta bayyana murnar ta ga waɗanda suka samu damar shiga shirin, sai dai ta ce, rukuni na ukun an raba shi zuwa kashi biyu, da ya haɗar da rukunin na uku zubin farko mai mutane dubu biyar da goma, sai rukuni na uku zubi na biyu mai mutane dubu huɗu da ɗari tara.

Hajiya Sadiya ta kuma ce, rukuni na uku zubin farkon an tsara bai wa waɗanda basu da takardar karatu, su dubu huɗu da hamsin, yayin da mutane dubu shida na rukunin za a dauki masu takardar karatu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!